Labarai
Dole masu ruwa da tsaki su amince da hukuncin kotuna -Sarkin Kano
Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya shawarci shugabannin hukomomi a matakai daban-daban da su amince da hukuncin da masu shari’a su ke zartarwa, da nufin samun dai-daito a tsakanin al’umma.
Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana haka ne yayin da yake karbar bakuncin tawagar mambobin kwamitin kula da harkokin shari’a na jihar Kano karkashin jagorancin shugaban kwamitin Malam Jamilu Shehu.
Sarkin ya kara da cewa talakawa suna da yakinin fatan samun adalci a kotuna, kasancewarsu wajen karshe da talaka zai samu adalci cikin sauk.
Tilas a magance cin zarafin mata- Mai dakin Sarkin Kano.
Sarkin Kano ya gana da masu zuba jari daga kasar Sin
Sarkin Kano ya gana da masu zuba jari daga kasar Sin
Shi ma na sa jawabin shugaban kwamitin Malam Jamilu Shehu, ya ce sun je fadar ne domin neman tabarriki da kuma shaidawa Sarki irin shirye-shiryen da kwamitin ke yi, wajen shawo kan matsalolin da kotunan ke fama da su a jihar Kano.
Wakilinmu na fada Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya ruwaito cewa Sarkin Kano ya nada sabon Dagacin ‘Dansango dake yankin karamar hukumar Kumbotso, Malam Muhammad Sani Isa.