Labarai
Dole ne a bai wa bangaren shari’a na jihohi cikakken ‘yanci – Majalisar Dattijai
Majalisar dattijai ta shaidawa gwamnonin kasar nan cewa, bai wa bangaren shari’a na jihohi cikakken ‘yancin sarrafa kudaden su lamari ne da ya zama dole da babu wanda zai canja shi.
Shugaban kwamitin kula da harkokin shari’a da kare hakkin bil adama na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce, abin kunya ne ace a wannan lokaci bangaren shari’a na jihohi na karkashin ikon gwamnonin, saboda haka majalisar dattijai za ta ci gaba da bai wa bangaren shari’a na jihohi goyon bayan da suke bukata don cimma muradun su.
A baya-bayan nan ne dai kungiyar ma’aikatan bangaren shari’a suka fara wani yajin aiki don nuna adawa da ci gaba da dakile bangaren shari’a na jihohi da su ke zargin gwamnoni na yi.
You must be logged in to post a comment Login