Labarai
Dole ne a rika sanar da damar daukar aiki a manyan makarantu- Ministan Ilimi

Gwamnatin tarayya, ta bai wa manyan makarantun gaba da Sakandare umarnin rika fitar da sanarwa a kafafen yada labarai duk yayin da suke shirin daukar sabbin ma’aikata
Ministan ilimi Dakta Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarni ta cikin wata sanarwa da Daraktat yada labaran ma’aikatarsa Folasade Boriowo, ta fitar a yau Alhamis.
Sanarwar, ta bayar da umarnin cewa ya zama wajibi makarantun su sanar a jaridar da za ta wallafa sanarwar ta karade kasar nan, sannan makarantun su wallafa sanarwar a shafukansu na Internet tare da kara yadawa a wasu kafafen.
Ministan ilimin, ya kara da cewa, ya dauki matakin ne domin tabbatar da adalci da dai-daito wajen daukar wadanda suka cancanta tare da sanya su a wuraren aikin da suka dace.
You must be logged in to post a comment Login