Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ladabtar da wadanda suka karya dokar hana amfani da shafin Twitter – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin kamawa tare da hukunta wadanda suka karya dokar haramata amfani da shafin tiwita a Najeriya.

Ministan shari’a kuma Atoni janar na tarayya Abubakar Malami ne ya bada umarnin.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Dr Umar Jibril Gwandu ya fitar ta bayyana cewa duk wanda aka kama da karya dokar zai fuskanci hukunci.

A juma’ar nan ne dai ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad ya sanar da dakatar da kamfanin tiwita daga aiki a Najeriya har sai abinda hali ya yi.

A sakamakon abinda kamfanin ya yi na goge wani jawabi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa yana gargadin masu tayar a hargitsi a kudancin kasar nan da su kuka da kansu, domin gwamnatin ba za ta nade hannu tana kallon suna kashe mutane haka kawai ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!