Addini
Dr. Rijiyar Lemo ya zama shugaban cibiyar shirya Muƙabala ta jami’ar Bayero
Jami’ar Bayero ta naɗa malamin nan Dr. Sani Rijiyar Lemo a matsayin sabon shugaban cibiyar wayar da kai da shirya muhawarorin addini na jami’ar.
Hakan ya biyo bayan amincewar shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas.
A yau Alhamis ne Dr. Rijiyar Lemo ya kama aiki, kamar yadda makusancinsa Dr. Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo ya wallafa ta shafinsa na Facebook.
Naɗin Dr. Sani Rijiyar Lemo na nufin ya maye gurbin tsohon shugaban cibiyar Farfesa Salisu Shehu.
Ayyukan da cibiyar ta ke, shi ne nazari kan al’amuran da suka shiga duhu ko a ka samu sarƙaƙiya a addini domin warware wa jama’a.
You must be logged in to post a comment Login