Kiwon Lafiya
Dr Sa’idu Ahmad Dukawa; an sami cigaba a demokradiya a kasar nan
Masanin nan kan harkokin kimiyyar Siyasa kuma Malami a Jami’ar Bayero da ke nan Kano Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa, ya bayyana cewar an samu ci gaba a Dimokoradiyyar kasar nan ta fannin tattalin arziki da tsaro, duk da cewar akwai yan rikice-rikice a cikin siyasar.
Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala Shirin Barka Da Hantsi na nan Freedom Rediyo na yau.
Sa’idu Ahmad Dukawa ya kuma ce rikicin da ke faruwa tsakanin jam’iyyun a Jihohin kasar nan ba zai haifar da wata matsala ga Dimokoradiyyar kasar nan ba, duba da yadda zabe ke gabatowa.
Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya shawarci shugabanin jam’iyyu da su yi duk abinda ya kamata wajen tafiyar da jam’iyyun na su, tare da gujewa haddasa rikice-rikicen da za su iya janyo zubar da jini yayin zabe don ganin an kara bunkasa Dimokoradiyyar kasar nan.
A na sa bangaren shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano Abdullahi Abbas cewa ya yi an samu ci gaba matuka a Dimokradiyyar a Jihar Kano da ma kasa baki-daya, inda ya bada misalin cewa a Kano shugaban Jam’iyyar yana samun girmamawar da ta kamata daga wajen gwamna da sauran mambobin Jam’iyya.