Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

DSS ta musanta hana iyalai da lauyoyin Emiefele ganawa da shi

Published

on

Hukumar tsaro ta DSS, ta musanta batun cewa, ta hana iyalai da lauyoyin dakataccen gwamnan babba bankin CBN Godwin Emiefele ganawa da shi.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ya fitar a karshen mako.

Sanarwar ta ce, Hukumar DSS na gudanar da aikinta ne bisa doka, don haka babu dalilin hana iyalai ko lauyoyi ko kuma likitoci ganin Mista Godwin Emefele don ya na tsare a hannunsu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da iyalan Emiefele suka shigar da ƙara Kotu inda suka nemi ta tilasta wa DSS ba da damar ganawa da shi.

Sai dai kotun ta amince da buƙatarsu inda ta umarci DSS ta bai wa dakataccen gwamnan babban bankinm damar gani da iyalai har ma da lauyoyi da kuma likitansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!