Manyan Labarai
DSS ta yi Awon gaba da shugabannin CRC a Kano kan zargin badakala
Wasu jami’an tsaro da ake kyautata zaton na farin kaya ne wato DSS sun cafke shugaban hukumar kula da ci gaban ilimi a matakin farko wato CRC na karamar hukumar Madobi Sunusi Shehu Yola da mataimakinsa Abdulkarim Jibril Kafin Agur, da kuma shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Surajo Usman Kubaraci.
an dai kama su ne sakamakon zarginsu da badakalar kudaden da gwamnatin tarayya ke bayarwa don ciyar da dalibai na kasar nan ciki har da nan Kano
Wata majiya mai tushe ta shaidawa Freedom Radio cewa an kama mutanen sakamakon zarginsu da amfani da karfin ikonsu wajen karbe kudin ciyarwar da aka sanyawa matan da ke aikin ciyarwar a asusunsu na bankuna, bayan da suka tilasta musu sannan suka karbe.
Mutanen sun tara matan ne tare da bayyana mu su kudurinsu, wanda kuma ana tsaka da taron ne sai jami’an tsaron suka dirar mikya a wurin tare da yin awon gaba da shugabannin.
Wasu daga cikin matan da ke aikin ciyarwar a wasu daga cikin makarantun Firamaren karamar hukumar Madobin, sun tabbatar da cewa ana karbar kudin a hannunsu.
Daya daga cikin iyayen yaran ya shaidawa Freedom Radio cewa lamarin ya jima yana faruwa inda kuma aka yi wa matan barazanar cewa matukar suka ki bayar da kudin, to za su rasa aikinsu na ciyar da daliban.
Wata majiya daga hukumar tsaro ta farin kaya DSS din ta tabbatar da cewa hakika mutanen suna hannunsu kuma suna amsa tambayoyi ne zangin sama da fadi da kudaden ciyar da daliban.