Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da manbobin ta guda 5

Published

on

Majaisar dokokin jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta guda biyar sakamakon zarginsu da tada hatsaniya a makon jiya.

A cewar majalisar dakatarwa wadda ta fara aiki nan ta ke, za ta kwashe tsawon watanni shida tana gudana.

Shugaban majalisar dokokin jihar ta Kano Abdul’aziz Garba Gafasa shi ya sanar da dakatar da ‘yan majalisar yayin zaman majalisar na yau.

Ya ce wadanda majalisar ta dakatar sun hada da,Alhaji Garba Ya’u Gwarmai mai wakiltar karamar hukumar Kunchi da Tsanyawa da Abdul Labaran Madari wakilin mutanen Warawa da Muhammed Bello Butu-Butu mai wakiltar karamar hukumar Tofa da Rimin-Gado.

Majalisar zartarwa ta Kano ta shiga taron gaggawa

A yau ne majalisar dattijai zata tabbatar sunayen ministoci bayan tantance su

Mutanen Ja’en za su yi karar majalisar dokokin Kano

Sauran sune, tsohon shugaban majalisar, Isyaku Ali Danja mai wakiltar karamar hukumar Gezawa da kuma Salisu Maje Ahmed Gwangwazo wakilin   birni da kewaye Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!