Labaran Kano
Duk da bayar da ilimi kyauta za’a cigaba da karbar kudin PTA- Inji Kungiyar PTA ta jahar Kano
Kungiyar iyayen yara da malamai ta jihar Kano tace zaa ci gaba da karbar kudin PTA duk kuwa da shirin bayar da ilimi kyauta da Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar.
Sakataren Kungiyar Iyayen yara da Malamai na Jihar Kano, Alhaji Aminu Tafida ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Duniyar Mu A Yau na tashar Freedom Rediyo, wanda ya mai da hankali kan batun ba da ilimi kyauta da Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar.
Alhaji Aminu Tafida, ya ce, babu gudu ba ja da baya, kan batun karbar kudin PTA kamar yadda sauran kasashen Duniya su ka dukufa wajen taimakawa harkokin ilimi.
Da ya ke ba da tasa gudunmawar a cikin shirin, Shugaban hukumar kula da Ilimin bai daya ta jihar Kano, Dr. Dallami Hayyo, cewa ya yi, matukar Iyaye basu yi tsayin daka kan harkar Ilimin ‘ya’yan su ba, musamman wajen cin gajiyar shirin ba da ilimi kyauta na gwamnatin jihar Kano, babu shakka, za a dade ana fama da koma baya a harkar ilimi a wanna yankin.
Wani tsohon Malamin makaranta da ya kasance cikin shirin Malam Ado Lawan Indabawa ya ce, shirin bada Ilimi kyauta da Gwamnatin Kano ta kaddamar abu ne mai kyau, amma akwai bukatar gyara ajujuwan dalibai da samar da isassun malamai da wadatattun kayan koyo da koyarwa.
Wakilinmu Abdulkarim Tukuntawa ya rawaito cewa Malam Ado Lawan Indabawa malamin yace, ko kadan bai amince da Gwamnati ta dauki ma’aikatan wucin gadi ba kasancewar hakan ka iya jawo tsaiko a cikin harkokin koyo da koyarwa.