Connect with us

Kiwon Lafiya

Duk da farfadowa da tattalin arzikin Najeriya ke yi cikin sauri amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba-IMF

Published

on

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ce duk da farfadowa da tattalin arzikin Najeriya ke yi cikin sauri amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba sakamakon talauci da ke ci gaba da addabar al’ummar kasar nan.

Asusun na IMF ya kuma bukaci mahukuntan kasar nan da su bullo da wasu sabbin sauye-sauyen tattalin arziki cikin gaggawa domin shawo kan matsalar da ke neman gagaran Kundila.

Hakan na cikin wani rahoto ne na faifan Video wanda da asusun na IMF ya fitar akan tattalin arzikin kasar nan a jiya.

Rahoton asusun ya kuma ce akwai bukatar amfani da tsarin tattalin arziki na gajeren zango wanda za a ga alfanunsa nan take maimakon tsarin  da zai dau tsawon lokaci.

Asusun na IMF ya ce akwai damuwa matuka ganin yadda kasar nan ke tunkarar babban zaben kasa a shekara mai zuwa a lokaci guda kuma da yakamata a ce hankalin gwamnati ya karkata wajen bullo da sabbin sauye-sauyen tattalin arziki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!