Connect with us

Labarai

IMF: Bashin wajen Najeriya zai kai Dala Biliyan 72.6 bayan zaben 2027

Published

on

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa bashin wajen Najeriya zai karu zuwa dala biliyan 72.6 nan da shekarar 2027, daga dala biliyan 51.9 da ake da shi a shekarar 2025. IMF ya danganta yiwuwar karin bashin da bukatun kashe kudi da kuma matsin tattalin arziki gabanin babban zaben kasar.

Rahoton ya bayyana cewa karin talauci, matsalar tsadar abinci da bukatun gwamnati na iya kara gibin kasafin kudi, lamarin da zai sa Najeriya ta ci gaba da neman karin lamuni daga kasashen waje. Haka kuma, IMF ya gargadi gwamnati kan wasu tsare-tsaren karbar bashi da ka iya jefa tattalin arzikin kasar cikin hadari.

Duk da haka, IMF ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar sun kara wa tattalin arzikin kasar karfi, tare da hasashen cewa GDP na Najeriya zai bunkasa da kashi 4.1 cikin dari a 2026 da kuma kashi 4.3 cikin dari a 2027.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!