Addini
Duk da gargadin Muhyi har yanzu ana samun tashin farashi a wasu kasuwannin Kano.
Yayin da aka shiga kwanaki hudu da fara azumin watan ramadan, rahotanni sun ce, har yanzu ana ci gaba da samun tashin farashin kayayyakin amfanin yau da kullum a wasu daga cikin kasuwanni da ke birnin Kano.
A ziyayar da freedom radio ta kai wasu daga cikin kasuwanni, ta gano cewa, kayayyaki musamman na masarufi farashinsu hauhawa ya ke karayi a ko da yaushe.
Misali a kasuwar sai da kayan marmari ta ‘yan lemo da ke Na’iba, a zantawar freedom radio da wasu daga cikin ‘yan kasuwar, sun ce, sukan sai da kayan ne kamar yadda suma suka samu.
Malam Murtala Yunusa shine jami’in hulda da jama’a na kasuwar, ya ce, yanayin rashin samun wadatar ruwan sama ne ya janyo karancin kayan marmarin.
Sai dai a kasuwar Tarauni, lamarin ya sha bamban da na kasuwar ‘yan lemo inda anan farashin ya sauko kasa da yadda aka saba saya kafin fara azumi.
You must be logged in to post a comment Login