Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Riga-kafin Corona: Ba a samu rasa rai ko daskarewar jini a Najeriya ba – WHO

Published

on

Gwamnatin tarayya da hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ce tun da aka fara yin allurar riga-kafin cutar corona ta Astrazaneca a Najeriya, ba a samu labarin rasa rai ko daskarewar jini ba.

 

Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko Dr. Faisal Shuaib ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a ranar juma’a a Abuja.

 

Sai dai a cewar sa, an samu labarin ciwon jiki, amai, gudawa, ciwon kai, kasala da zazzabi da dan sauran wasu kunji-kunji a wasu jihohi biyar.

 

Jihohin da aka fi samu korafin sun hada da: Lagos, Kaduna, Yobe, Kebbi da kuma Cross River.

 

An dai fara allurar rigakafin ta Astrazaneca a Najeriya a ranar goma sha biyar ga watan jiya na Maris.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!