Connect with us

Labarai

Duk da hatsaniyar da ta faru, karshe gwamnan Gombe ya nada Danladi Sanusi a sarautar Mai Tangale

Published

on

Gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya nada Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon Mai Tangale.

Nadin nasa na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe Isma’ila Uba Dan Misili.

Sanarwar ta ruwaito gwamnan na cewa, kamar yadda dokar nadi da sauke sarakunan gargajiya ta jihar Gombe ta shekarar dubu biyu da ashirin ta zayyana, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya nada Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon basaraken kasar Tangale.

Sanarwar ta ruwaito kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiyar na jihar Gombe Ibrahim Dasuki Jalo na bayyana amincewar gwamnan wajen nadin Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sarautar Mai Tangale.

Kwamishinan ya kuma mikawa sabon basaraken kasar ta Tangale wasikar nadin nasa a gidansa da ke Poshiya a karamar hukumar Billiri.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!