Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Duk gidan sayar da abinci ko Biredi da bashi da shaidar lafiya ku rufe shi – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bai wa hukumar kare hakkin masu sayen kaya ta jihar umarnin rufe dukkanin gidajen abinci da na Biredi da kuma kamfanonin samar da ruwan sha da aka samu suna aiki ba tare da shaidar amincewa daga ma’aikatar lafiya ba.

Shugaban hukumar Baffa Babba Dan’agundi ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi bayan karewar wa’adin da aka bai wa masu sarrafa abinci da na sha su yi rajista da ma’aikatar lafiya.

Baffa Babba ya ce, ya zama dole a dauki matakin, sakamakon yadda hukumar ta samu wasu gidajen abinci da ma’aikatan su ke fama da ciwon hanta kuma suna mu’amala da jama’a.

Baffa ya ce, hukumar ba zata zuba idanu tana ganin yadda ake sakaci da lafiyar al’ummar jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!