Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ko ‘Da na ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da shi ba zan basu kudin fansa ba – El-Rufai

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce, ko da dansa ‘yan bindiga suka sace su ka yi garkuwa da shi, ba zai taba basu kudin fansa domin su sake shi ba.

Gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne a yau juma’a yayin zantawa da manema labarai.

A cewar sa, ya sha fada zai kuma fada ko da dansa ne aka sace aka yi garkuwa da shi, ba zai biya kudin fansa ba.

A cewa gwamnan na Kaduna maimakon ya biya kudin fansa ga ‘yan bindiga su saki dan nasa, gara ya yi masa addu’ar cikawa da Imani.

Ya kuma ce har yanzu gwamnatinsa tana kan bakarta ba za ta biya kudin fansa don ‘yan bindiga su saki daliban kwalejin nazarin sirrai da gandun daji ta Kaduna wadanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a kwanakin baya ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!