Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dukkanin kafofin yada labarai su gaggauta rufe shafukan su na Twitter – NBC

Published

on

Dukkanin kafofin yada labarai su gaggauta rufe shafukan sun a Twitter – NBC
Hukumar kula da kafofin yada labari ta kasa NBC, ta umarci kafafen yada labarai da su gaggauta rufe shafukansu na Twitter.

Mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar Ekanem Antia, ne ya bayyana hakan a yau Litinin.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa hukumar ta bada umarnin ne biyo bayan dakatar da amfani da shafin na Twitter da gwamnatin tarayya ta yi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta dakatar da amfani da shafin, biyo bayan goge wani rubutu da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kan masu tayar da kayar baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!