Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hatsarin Kwale-kwale- Mun gano mutane 97 cikin 160 – Gwamna Bagudu

Published

on

Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da gano gawarwaki kimanin 97 cikin wadanda hadarin jirgin kwale-kwale ya rutsa da su makwanni biyu da suka gabata.

Gwamna Abubakar Bagudu ya bayyana hakan ne a birnin Kebbi lokacin da yake karbar bakuncin tawagar yan majalisar wakilai da suka je yi masa ta’aziyyar mutumar mutanen da hatsarin ya rutsa da su.

Bagudu ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin lalubo ragowar da lamarin ya rutsa da su.

Idan za a iya tunawa tun a ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata ne jirgin kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji da masu hakar zinare sama da 160 ya nutse a yankin Warrah da ke karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!