Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babu wani dalibina da ya rasu a hannun yan bindiga – shugaban makarantar Tegina

Published

on

Shugaban makarantar Islamiyyar nan ta garin Tegina a karamar hukumar Rafi ta jihar Niger da aka yi garkuwa da dalibanta Malam Abubakar Alhassan, ya musanta rahoton da ke cewa wasu daliban sun rasu.

Malam Abubakar Alhassan ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martani kan labarin dake yawo a kafafen sada zumunta da ma wasu kafafen yada labarai a kan lamarin.

Ya ce, ko a daren Lahadin nan yayi magana da daya daga cikin malaman da ke cikin daliban da aka sace, inda ta tabbatar da cewa dukkanin su suna cikin koshin lafiya.

“Ana samun ci gaba wajen tattaunawa da ‘yan bindigar dajin, ta yadda ake samun ragin kudaden da suka nema don fansar daliban” a cewar shugaban makarantar.

Malam Abubakar ya kara da cewa,akwai fahimta tsakanin su da yan bindigar don kuwa sun tabbatar da cewa ba za su azabtar da su ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!