Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

ECOWAS ta baiwa Goodluck mukami

Published

on

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta nada tsohon shugaban kasar nan Goodluck Ebele Jonathan a matsayin Jakada na musamman wanda zai sasanta rikici a kasar Mali.

Wannan na cikin wata Sanarwar mai dauke da sa hannun mataimakin kan harkokin yada labarai, Ikechukwu Eze.

A cewar sanarwar, an nada tsohon shugaban ne domin tattaunawa da bangarorin da ke rikici a Mali da zummar sasanta su don samar da zaman lafiya.

Ta cikin sanarwar, ana bukatar Jakadan na musamman ya gana da shugaba Ibrahim Boubacar Keita da kuma bangarorin ‘yan adawa da kungiyoyin fararen hula a ziyarar da zai kai kasar.

Jonathan ya godewa kungiyar da kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan goyan bayan da ya bashi wajen bashi jirgin saman gwamnati da kuma duk abinda yake bukata domin samun nasarar aikin dake gaban sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!