Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan takarar shugabancin WTO za su bayyana gaban mambobin kungiyar

Published

on

A cikin wannan makon ne ‘yan takarar neman zama babban daraktan kungiyar cinikin ta duniya, WTO su takwas daga nahiyoyin hudu na duniya za su bayyana gaban mambobin kungiyar don bayyana irin manufofin da suke da su kan ciyar da kungiyar gaba.

Bayan wuce matakin fitar da ‘yan  takarar da aka kammala ranar 8 ga wannan wata na Yuli, ‘yan takarar, maza biyar da kuma  mata uku, za su bayyana gaban  mambobin kungiyar su 164 tun daga yau Laraba 15 ga wata zuwa jibi Juma’a 17 ga wata.

‘Yan takarar ,wadda daya daga cikin su ita ce tsohuwar ministar kudin Najeriya, Misis Ngozi Okonjo Iweala, wadda kuma Najeriyar ce ta tsayar da ita takarar zaben na neman karbar ragamar shugabancin kungiyar ne daga shugaban na yanzu, Roberto Azevedo da ke shirin ajiye mukamin nasa ranar 31 ga watan Agusta mai kamawa.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Abdel-Hamid Mamdouh, dan  kasar Masar da Amina Mohammed, ‘yar kasar Kenya da Jesus Kuri, dan Mixico da Tudor Ulianovschi, dan kasar Moldova da Yoo Myung-hee, dan kasar Korea da Mohammed Al-Tuwaijri dan kasar Saudi Arebiya da kuma Liam Fox dan kasar Birtaniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!