Labarai
ECOWAS za ta yi taro bisa ficewar Nijar Mali da Burkina Faso daga kungiyar

Kungiyar tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta yamma, ECOWAS, ta bayyana cewa za ta gudanar da taro na musamman, kan ficewar ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso daga ƙungiyar.
A cewar ECOWAS ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, za ta yi taron ministocin ƙungiyar ne a Accra, babban birnin ƙasar Ghana.
BBC, ta ruwaito cewa, wasu majiyoyi sun ce taron zai tattauna hanyoyin ficewar ƙasashen daga ƙungiyar da kuma tasirin hakan a kan hukumomi da cibiyoyin ƙungiyar da ke ƙasashen uku.
You must be logged in to post a comment Login