Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

EDO 2020: An killace ‘yan wasa 10 da suka kamu da Corona

Published

on

An killace kimanin ‘yan wasa goma da aka samu dauke da cutar Corona yayin da ake tsaka da gudanar da gasar bikin kakar wasanni ta 2020 a jihar Edo.

Yayin tattaunawa da manema labarai babban jami’in kwamitin dakile yaduwar cutar Corona Dakta Andrew Obi, ya ce, an mika bakwai daga cikin masu dauke da cutar zuwa wajen killacewa a asibitin Stella Obasanjo dake jihar ta Edo.

Ya kuma ce, sauran ‘yan wasan uku ba a kaiga mika su asibitin ba amma tuni aka killace su.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, “Za a cigaba da kula da ‘yan wasan da suka kamu da cutar har sai sun warke kafin su dawo cikin mutane kamar yadda Dakta Obi ya bayyana.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!