Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Edo 2020: ‘Yan sanda sun kwantar da hatsaniyar magoya baya da ‘yan kallo

Published

on

An samu hatsaniya a dakin wasan damben “Kick Boxing” bayan da aka umarci ‘yan wasa da magoya baya su fice daga dakin wasan domin kare dokokin hana yaduwar Corona.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gudanar a gasar kakar wasanni ta 2020 a jihar Edo.

Hatsaniyar ta farune a lokacin da ‘yan kallon suka cika dakin da ake gudanar da wasan Damben lamarin da ya sanya take dokokin dakile yaduwar cutar Corona.

Wakilan masu shirya gasar sun nemi dauki daga wajen jami’an ‘yan sanda yayin da suka gaza daidaita hatsaniyar magoya baya da kuma ‘yan kallon dake dakin wasan.

Daga bisani jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar kwantar da hatsaniyar don cigaba da gudanar da wasannin a tsanake.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!