Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

JUSUN: Ma’aikatan shari’a a Najeriya za su tsunduma yajin aiki

Published

on

Kungiyar ma’aikatan shari’a ta kasa reshen jihar Kano (JUSUN) ta ce za ta rufe dukkanin kotuna da ma’aikatun shari’a a kasar nan daga ranar 6 ga watan Afrilun 2021.

Hakan na cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar na kasa reshen jihar Kano, Mukhtar Rabi’u Lawan, ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan umarnin da uwar kungiyar ta kasa ta bayar, tun a ranar daya ga watan da muke ciki na Afrilu kan tafiya yajin aikin.

Hakan kuma ya sanya kungiyar a nan Kano ke umartar dukkanin membobinta da suyi biyayya ga umarnin uwar kungiyar kan batun zama a gida tare da rufe dukkanin kotuna da ma’aikatun shari’ar daga ranar shida ga watan Afrilun.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!