Connect with us

Labarai

Edo 2020: Za a cigaba da gasar kamar yadda aka tsara – Dare

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin cigaba da gudanar da gasar kakar wasanni ta 2020 da a yanzu haka ake tsaka da aiwatarwa a jihar Edo.

Umarnin na zuwa ne jim kadan bayan da kwamitin shirya gasar na jihar ta Edo ya bayyana dakatar da gasar sakamakon rashin kudaden gudanarwa.

Mataimakin daraktan yadda labarai a ma’aikatar wasanni ta kasa Ramon Balogun ne ya bayyana matsayar gwamnatin tarayyar kan sha’anin gasar.

Balogun ya ce “Ma’aikatar ta tabbata da ce ana cigaba da gudanar da gasar kuma wasanni na tafiya kamar yadda aka tsara.”

‘Yan wasa dai sama da dubu takwas ne daga jihohin daban-daban a fadin kasar nan suke fafatawa a bikin kakar wasannin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives