Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

EFCC shipyard Sokoto ta kama shugaban kungiyar manoman shinkafa na karakamar hukumar Gumi

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar Sokoto, ta ce, ta kama shugaban kungiyar manoman shinkafa reshen karamar Hukumar Gumi da ke jihar Sokoto Alhaji Ibrahim Rijiya, sakamakon zargin sa da laifin karkatar da taki da kuma wasu magungunan kwari da gwamnati ta samar domin amfanin manoma.

 

Haka zalika EFCC ta kuma ce ta kama babban jami’I da ke kula da ajiyar kayayyaki na karamar Hukumar ta Gumi, Aminu Musa da kuma wani mutum mai suna Abdullahi Bashir, sakamakon zarginsu da hadin baki wajen karkatar da takin da magungunan kwari.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun Hukumar ta EFCC Tony Orilade.

 

Sanarwar ta ce, mutanen uku sun hada baki wajen karkatar da motocin dakon kaya guda uku makare da takin zamani buhu dubu daya da dari takwas da kuma magungunan kwari wanda gwamnati ta samar domin amfanin manoman shinkafa a yankin.

 

A cewar sanarwar da mai magana da yawun Hukumar ta EFCC Tony Orilade ya fitar, shugaban manoman shinkafar karamar Hukumar ta Gumi Alhaji Ibrahim Rijiya, wanda kuma shine hakimin kasar ta Gumi, bayan karkatar da takin ya rika sayarwa akan kudi naira dubu uku-uku.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!