Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NEMA ta fara raba tallafi ga manoman da ambaliyar ruwa ya shafa a 2020 a jihar Sokoto

Published

on

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta fara rabon kayan tallafin noma ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2020 a jihar Sokoto.

Tallafin dai wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rabawa, ƙarƙashin asusun tallafawa manoma na gwamnatin tarayya.

Shugaban hukumar Mustapha Habib wanda shugaban sashin bincike da kuma kai ɗauki Malam Aminu Ambursa ya wakilta a wajen rabon tallafin ya ce, za su tabbatar an miƙa tallafin ga waɗanda lamarin ya shafa a ƙananan hukumomi kamar haka:

Ƙananan hukumomin Bodinga, Binji, Dange-Shuni, Ilella, Isa, Gada, Goronyo Gwadabawa, Kebbe, and Rabah.

Sauran su ne, Sabon Birni, Shagari, Silame, Tambuwal, Tureta, Wurno da Wamakko.

Kayan tallafin da aka raba kuwa sun haɗar da bututun ban ruwa takin zamani irin Shinkada Masara Gyaɗa  da magungunan kashe ƙwari da sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!