Connect with us

Labarai

Wasu magungunan kwari da manoma ke amfani da su na da illa ga lafiyar dan Adam

Published

on

Wani masani kuma mai bincike a fannin magungunan kwari da ke sashin nazarin tsirrai a  jami’ar Bayero da ka nan Kano ya bayyana magungunan kwari da manoma ke amfani da su da cewa na daya daga cikin abubuwan da suke haifar da illa ga lafiyar jikin dana dam.

Alhaji Murtala Ya’u ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na tashar freedom Radio a safiyar yau.

Ya kara da cewa daga cikin illolin da magungunan ke haifarwa akwai cutar ciwon koda ciwon Hanta,wanda suna daya daga cikin cutukan da mutane ke fama da su a yanzu.

A nasa bangaren sarkin Noma na jihar Kano Alhaji Yusuf Na-Dabo yace rashin kula da yadda za’ayi amfani da magugunan na daya daga abinda yake kawo gurbacewar kayayyakin noma.

Bakin biyu sun bukaci manoma da su rinka baiwa gona hutu na dan lokacin wanda hakan yana taimakawa wajen samun kyakyawan amfani gona

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,262 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!