Labarai
EFCC ta cafke mutane 26 da ake zargi da damfara ta Internet
Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar birnin Fatakwal ta ce, ta cafke mutane 26 da ake zargi da damfara ta kafar internet.
Hukumar ta EFCC ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shifinta X.
EFCC ta ce, an kama mutanen ne sakamakon sahihan bayanan sirri kan zargin da ake musu na hannu a ayyukan da suka shafi damfara ta internet.
Haka kuma ta ce, kayayyakin da aka ƙwace a hannun su sun haɗa da wayoyin hannu da kwamfutoci da motocin alfarma guda 6.
Ta cikin sanarwar, hukumar ta kuma bayyana cewa, za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kansu.
You must be logged in to post a comment Login