Labarai
EFCC ta fara shirin gurfanar da Murja Ibrahim Kunya a Kotu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta ce, ta shirye-shiryen gurfanar da Murja Ibrahim Kunya a gaban kotu bayan da ta sake cafke ta sakamakon tserewar da ta yi bayan da hukumar ta bayar da ita beli tun a watan Janairun bana.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a ya Litinin ta na mai cewa a baya ta bayar da Murja beli ne gabanin gurfanar da ita a gaban babbar kotun tarayya, amma sai ta tsere.
Haka kuma, sanarwar ta kara da cewa, tun a cikin watan Janairu ne hukumar ta kama Murja Kunya bisa zarginta da wulakanta takardun kudi, wanda hakan ya saba da dokar babban bankin kasa CBN.
You must be logged in to post a comment Login