Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta bayar da belin Murja Kunya

Published

on

Babbar Kotun jiha a nan Kano da ke zamana a Bompai ta bada Belin fitacciyar mai amfani da shafin nan na TikTok Murja Ibrahim Kunya.

Kotun karkashin mai Shari’a Nasiru Saminu ce ta bada Belin nata a yau Litinin, bayan bincika wasu dokoki da suka kafa hukumar Hisba wanda zai iya bada belin nata.

Matakin bayar da belin ta biyo bayan hutun da kotun zata tafi, inda ta sanya sharadi ga Murja Ibrahim Kunya na daina wallafa komai a shafukan ta na sada zumunta har sai an kammala Shari’a.

Haka kuma, kotun ta bukaci murja ta kawo mutane biyu da za su tsaya mata, har ma ta umarci Kwamishinan yan sanda na Kano ya sanya ido kan Murja Kunya don ganin bata karya doka ba.

yanzu haka dai Murja Ibrahim Kunya ta shafe tsawon kwanaki 35 cikin tuhumar da ake yi mata, wadda ta kai ga bincikar lafiyarta ƙwaƙwalwarta.

 

Rahoton: Madina Shehu Hausawa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!