Labarai
EFCC ta mika wa gidan rediyo muryar Najeriya kadarar da ta kwace
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (EFCC), ta mikawa gidan rediyon muryar Najeriya (VON), kadarar da ta kwace daga hannun tsohon babban hafsan tsaron kasar nan marigayi Air Chief Marshal Alex Badeh.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin jami’in yada labarai na Hukumar ta EFCC Tony Orilade.
Sanarwar ta ce ginin da ke kan fuloti mai lamba dubu daya da dari uku da tamanin da shida da ke Uda Crescent a Unguwar Wuse 2 a Abuja, a yanzu ya zama sabon shalkwata ta gidan rediyo muryar Najeriya.
A cewar sanarwar mai rikon mukamin shugaban Hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ne ya mika makullin ginin ga gidan rediyon na muryar Najeriya.
Ta cikin sanarwar dai an kuma ruwaito Ibrahim Magu na kira ga al’ummar kasar nan da su rika taimakawa Hukumar da bayanai domin kawadda ayyukan cin hanci daga kasar nan.