Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

#EndSARS : Yadda Dattawan Arewa suka nemi masu bore su dena zanga-zanga

Published

on

Kungiyar dattawan arewa ta northern elders forum ta shawarci masu gudanar da zanga-zangar rushe ‘yan sandan SARS da su kawo karshen boren da suke yi.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai magana da yawun kungiyar Dr Hakeem Baba Ahmed.

Tun a ranar shida ga wannan wata ne matasa suka fantsama kan tituna a kasar nan suna zanga-zangar neman ganin kawo karshen cin zarafin jama’a da ‘yan sandan na SARS ke yi.

A cewar kungiyar dattawan arewa ta northern elders forum din, yanzu wasu sun fake da zanga-zangar don biyan wasu boyayyen bukatunsu.

Haka zalika kungiyar ta NEF ta kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnonin kasar nan talatin da shida da su saurari masu zanga-zangar don basu tabbacin cewa matsalolin da suke zanga-zanga akai za a kawo karshensa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!