Labarai
#EndSARS : Yadda Ganduje ya gana da kungiyoyi masu zaman kan su
Da yammacin jiya ne gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gana da shugabannin kungiyoyi masu zaman daban-daban kan abinda ke faruwa a kasar nan na zanga-zangar EndSARS da kuma yadda za’a tabbatar da Zaman lafiya a nan Kano.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da su baiwa gwamnatin gudunmawa na ganin cewa wani rikici bai barke ba anan Kano, musamman wajen tabbatar da samun fahimtar juna da samun hadin kai a tsakanin al’umma.
Jim kadan bayan gama Jin raayoyin kungiyoyi ne daga cikin bayanan gwamnan ya ce zai kafa kwamitin da zai bada dama ga kungiyoyin al’umma da masu zaman kansu wajen ganawa da hukumomi masu zamna kansu wajen tabbatar da bin kaidoji ya yin daukar aiki
Muhammad Mustafa Yahya shi ne mataimakin shugaban gamayyar kungiyon fararen hula na Kano ya bayyana ra’ayinsa akan yadda gwamnatin Kano zata bi wajen kaucewa tashe-tashen hankula yayin da yake zantawa da manema labarai.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da dama sun bayyana ra’ayoyin su tare da jan hankalin gwamnati kan hanyoyin da ya kamata abi don tabbatar da zaman lafiya a nan Kano.
You must be logged in to post a comment Login