Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

#EndSARS : Yadda Ganduje ya gana da kungiyoyi masu zaman kan su

Published

on

Da yammacin jiya  ne gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gana da shugabannin kungiyoyi masu zaman daban-daban kan abinda ke faruwa a kasar nan na zanga-zangar EndSARS da kuma yadda za’a tabbatar da Zaman lafiya a nan Kano.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da su baiwa gwamnatin gudunmawa na ganin cewa wani rikici bai  barke ba anan Kano, musamman wajen tabbatar da samun fahimtar juna da samun hadin kai a tsakanin al’umma.

Jim kadan bayan gama Jin raayoyin kungiyoyi ne daga cikin bayanan gwamnan ya ce zai kafa kwamitin da zai bada dama ga kungiyoyin al’umma da masu zaman kansu wajen ganawa da hukumomi masu zamna kansu wajen tabbatar da bin kaidoji ya yin daukar aiki

Muhammad Mustafa Yahya shi ne mataimakin shugaban gamayyar kungiyon fararen hula na Kano ya bayyana ra’ayinsa akan yadda gwamnatin Kano zata bi wajen kaucewa tashe-tashen hankula yayin da yake zantawa da manema labarai.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da dama sun bayyana ra’ayoyin su tare da jan hankalin gwamnati kan hanyoyin da ya kamata abi don tabbatar da zaman lafiya a nan Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!