Labaran Wasanni
Erik ten Hag ya zama sabon mai horar da Manchester United
Erik ten Hag zai jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a kakar wasanni mai zuwa.
Tawagar ce dai ta sanar da nadin sabon mai horarwar a ranar Alhamis 21 ga Afrilun 2022.
Mai shekara 52 ya amince da sanya hannu a kwantaragin shekaru 3 a kungiyar.
Dan kasar Holland ya zama mai horarawa na biyar da zai kasance a filin Old Trafford tin bayan da Alex Ferguson ya yi murabus a kungiyar a shekara 2013.
Ten Hag shi ne mai horar da Ajax, inda ya jagoranci kungiyar lashe gasar Red Devilsand.
Yanzu haka Ralf Rangnick shi ne ke rike da kungiyar a matsayin na rikon kwarya, kafin daga bisani ta sanar da sabon mai horarwa da zai kasance a kakar wasannin shekarar 2022/2023.
Manchester United dai na mataki na 6 a gasar Firimiya da maki 54 wadda ta ke yunkurin kasancewa cikin kungiyoyin da zasu wakilci kasar a gasar cin kofin zakarun turai.
You must be logged in to post a comment Login