Labarai
EU ta sanya wa Rasha sabbin Takunkumai bisa yakinta da Ukraine
Kungiyar tarayyar Turai EU, ta amince da sanya sabbin takunkumai ga kasar Rasha da dukkan masu hannu a yaƙin da kasar ke yi da kasar Ukraine.
Haka kuma, a karon farko, ƙungiyar ta amince da sanya takunkumi a kan kamfanonin China masu bai wa Rasha kayan yaki musamman ma jirgin sama marar matuƙi da sauran kayan lantarki.
Takunkumin ya haɗa da ɗaukar ƙwararan matakai a kan kamfanonin India da Serbia da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Kafar yada labarai ta BBC, ta ruwaito cewa, kungiyar ta kuma sanya takunkumi a kan jami’an Koriya ta Arewa biyu, da dakarun Rasha da suka kai harin rokoki kan asibitin yara a Ukraine, a cikin watan Yulin da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login