Labaran Wasanni
Euro 2020: Ronaldo ya kamo Ali Daei a tarihin zura kwallaye 109

Cristiano Ronaldo ya daidaita tarihin zakarun ‘yan wasan duniya wajen cin kwallaye 109 bayan cin kwallaye biyu a wasan da Portugal ta fafata da Faransa a gasar Euro 2020.
Dan wasan mai shekaru 36 ya yi daidai da Ali Daei dan kasar Iran kuma yanzu haka ya ci kwallaye biyar a gasar ta bana.
Ronaldo ya riga ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a gasar cin kofin nahiyar turai inda ya samu adadin kwallaye 14.
Idan har Portugal ta ci gaba jan zaranta, Ronaldo zai kasance a shirye don lashe kyautan takalmin zinarai ta bana.
You must be logged in to post a comment Login