Labarai
Fadar shugaban ƙasa ta caccaki Atiku

Fadar Shugaban Ƙasa ta soki tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, bisa kalaman sa na cewar ’yan Najeriya na fama da yunwa da kuma tashin hankali, da ya kwatanta halin da ake ciki a kasar da juyin juya halin Faransa na 1789 da na Rasha na 1917.
Mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkar yada labarai Bayo Onanuga, ya ce maganganun na Atiku ba daidai ba ne, kasar na samun ci gaba a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.
Hadimin ya kafa misali da yadda bayanan Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa NBS da suka nuna farashin kaya na sauka tsawon watanni biyar a jere, da ya ce ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma zargi Atiku da jam’iyyar PDP da yaɗa maganganun da za su kawo tashin hankali, da ta bayyana cewa yawancin matsalolin da ake fuskanta sun samo asali ne daga rashin kyakkyawan shugabanci tun a lokacin PDP, lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login