Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai jihar Bauchi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma babban birnin tarayya Abuja bayan ziyarar kaddamar da wasu ayyuka da ya kai jihar Bauchi.

A yayin ziyarar ta shugaba Buhari ya kai zuwa jihar Bauchi ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta samar, ciki har da Asibitin sojojin sama.

Ya kuma kaddamar da shirin tallafawa manoman jihar da kayayyakin aikin noma.

Shugaba Buhari dai ya isa jihar ta Bauchi a safiyar jiya Alhamis, inda ya sauka a filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar ta Bauchi, yayin da ya samu tarba daga gwamnan jihar ta Bauchi Muhammad Abubakar da kuma gwamnan jihar Adamawa Mohammed Jibrilla.

Ministan Tsaro Birgediya Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya da Babban Hafsan Tsaron kasar nan Janar Abayomi Olanisakin, da sauran kusoshin gwamnatin na cikin wadanda suka yiwa shugaban Kasa Rakiya a yayin ziyarar tasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!