Labarai
Fadar shugaban kasa ta bukaci a gaggauta bincikar El-Rufa’i

Fadar shugaban Najeriya ta yi kiran gudanar da cikakken bincike kan iƙirarin da tsohon gwamman jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi game da suna kutse a kayin wayar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da sauraron wayarsa.
Cikin wata hira da El-Rufai ya yi da wani gidan talbijin a ƙasar ranar Juma’a, ya yi iƙirarin cewa yana sane da batun yunƙurin kama shi da aka yi lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Abuja ranar Alhamis.
El-Rufai ya zargi Nuhu Ribadu da bayar da umarnin kama shi, inda ya ce ya ji wayar da Nuhu Ribadu ya yi lokacin da yake bayar da umarni, bayan da wasu suka yi masa kutse tare da sauraron wayar.
To sai dai kakakin shugaban Najeriya, Bayo Onanuga cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana iƙirarin El-Rufai a matsayin amsa laifi, tare da aza ayar tambayar cewa ko tsohon gwamnan da mutanen da ke masa aikin na da damar yin hakan.
”Ya kamata a yi cikakken bincike game da batun a kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi, saboda ba wanda ya fi ƙarfin doka”, a cewar Bayo Onanuga.
You must be logged in to post a comment Login