Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An samu raguwar rashin tsaro cikin mako 2- Ribadu

Published

on

Babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya yi iƙirarin cewa rashin tsaro ya ragu cikin mako biyu, bayan naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron Nijeriya.

Malam Nuhu Ribadu, wanda ya yi wannan furuci bayan wata ziyara da hafsoshin tsaron suka yi wa shugaba Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

Ya kuma ce, hakan ta tabbata ne saboda ƙwararrun da aka zaɓa a matsayin masu jagorantar sha’anin tsaron.

Haka kuma ya kara da cewa sun ziyarci shugaban ƙasar ne domin su nuna godiya da damar da aka ba su, ta bayar da irin tasu gudunmawar wajen ci gaban ƙasa, kuma za su yi aiki tukuru waje tabbatar da ingantaccen tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!