Kiwon Lafiya
Fadar shugaban kasa ta musanta umarnin kama Amaju Pinnick
Fadar shugaban kasa ta musanta batun da ke yawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada Umarnin kamawa tare da gurfanar da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa Amaju Pinnick.
Rahotanni sun bayyana cewa fiye da sa’o’I 24 kenan da labarin ya fara yawo cewa akwai babbar barazana da ke fuskantar hukumar ta kwallon kafa, inda ake yadawa cewa shugaban Buhari ya bada umarnin chafkewa da kuma gurfanar da shi gaban kotu kan zargin cin hanci da rashawa.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai malam Garba Shehu, ya fitar a Abuja ta bayyana cewa wannan labari bashi da tushe ballantana makama.
Garba Shehu ya kuma ce duk wanda ya san shugaba Buhari ya sanshi da bin doka da oda, adon haka babu yadda za’a yi shugaba Buhari ya dauki wannan mataki kai tsaye.
Daga nan kuma sai ya yi kira ga al’umma da su yi watsi da wannan batu.