Connect with us

Kiwon Lafiya

An nada kwamandojin da ke ba da umarnin mayakan boko haram

Published

on

Babban hafsan tsaron kasar nan Laftanar janar Tukur Buratai ya nada sabbin manyan kwamandoji da ke bada umarnin ga rundunonin hukumar na musamman wadanda ke yaki da mayakan Boko Haram.

Wannan nadin dai ya biyo bayan umarnin da ministan tsaron kasar nan Mansur Dan-Ali ya bayar, na cewa a sauya fasalin rundunar Operation Lafiya Dole don samun cikakkiyar nasarar da ake bukata a yakin da suke yi a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labaran Rundunar Brigediya Janar Sani Usman ya fitar ta bayyana cewa an yi hakan ne don shigo da sabbin jini cikin al’amarin tabbatar da tsaro a kasar nan, inda kuma yace cikin gyaran da aka yi ya hadar da sauyin guraren aiki ga manyan jami’an hukumar da kuma Karin girma ga wasu.

Cikin wadanda aka yiwa Karin girman akwai OT Akinjobi wanda shine shugaban sashin da ke sanya ido na rundunar, wanda aka karawa girma zuwa kwamandan sashi na uku na rundunar Operation Lafiya Dole da sauran su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,677 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!