Labarai
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cewar za ta sauke shugaban hukumar INEC
Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sadamunta da ke cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sauke shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC) Farfesa Mahmud Yakubu daga mukaminsa sakamakon dage zaben ranar Asabar da ta shige.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya ce, zancen ba gaskiya bane, kuma shugaban kasa ba yi da wani shiri na yin hakan.
A cewar sa, zance ne kawai da wasu suka kitsa amma babu wani shiri na sauke shugaban hukumar INEC a wannan lokaci.
Malam Garba Shehu ya ma kalubalanci masu yada labaran da ya bayyana su a matsayin masu yada karairayi da cewa, su je su duba kundin tsarin mulkin kasar nan irin bayanan da ya yi kan nadin shugaban hukumar zabe da kuma yadda ake sauke shi.
Rahotanni sun yi ta yawo a kafafen sada zumunuta da ke ruwaito wasu manyan ‘yan siyasar kasar nan na cewa shugaba Buhari na shirin sauke shugaban hukumar ta INEC sakamakon sauya lokacin gudanar da zaben.
Wannan na zuwa ne kuma a lokaci guda da rahotanni ke cewa shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmud Yakubu, ya karbi ragamar aikin rarraba kayayyakin zabe da kanshi domin gujewa fuskantar matsala a nan gaba.