Kiwon Lafiya
Fadar shugaban kasa ya mayar da martani ga shugaban cocin Katolika
Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga kalubalantar da shugaban Cocin Katolika shiyyar Yola Stephen Mamza ya yi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa, ba ya yin abinda ya da ce, kan rashin tsaro da ke addabar kasar nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.
Ta cikin sanarwar, fadar shugaban kasa, ta zargi shugabannin al’umma da laifin kara rura wutar rikice-rikice da ake samu a sassa daban-daban na kasar nan.
A cewar Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar dai, gwamnatin shugaba Buhari ta na aiki dare ba rana don tabbatar da tsaro da kuma rayukan al’umma.
A baya-bayan nan ne dai shugaban Cocin Katolika Shiyyar Yola Stephen Mamza, ya zargi shugaban kasa da rashin katabus game da yawan rikice-rikice da ake samu a kasar nan.