Labarai
Farashin ɗanyen man fetur ya sake haura sama da dala 100

Farashin ɗanyen man fetur ya sake haura sama da dala 100 kan kowacce ganga guda, bayan ya yi ƙasa sosai a jiya Litinin.
A kasuwannin nahiyar Asiya da safiyar yau Talata, farashin fetur ya ƙaru da kaso sama 3 da digo 75 zuwa dala 103 da digo 69.
Rahotonni sun bayyana cewa, a jiya Litinin farashin man ya faɗi da fiye da kaso 10 bayan da Donald Trump ya ɗage shirin kai hare-hare kan tashoshin lantarkin Iran bayan ya ce ya tattauna da Iran lamarin da Iran din ta musanta.
You must be logged in to post a comment Login