Kiwon Lafiya
Farashin gangan danyen man ya tashi a kasuwar Brent da ke birnin London
Farashin gangan danyan mai ya tashi a kasuwar Brent da ke birnin London zuwa dala 83 da santi 27.
Sai dai a kasuwar West Texas Intermediate da ke kasar Amurka farashin ya ci gaba da kasancewa akan dala 73 da santi 57.
Rahotanni sun ce wannan shine hauhawan farashi mafi girma cikin shekaru hudu da suka gabata.
Masu sharhin lamuran yau da kullum sun alakanta hauhawan farashin da barazanar sanya takunkumi da kasar Amurka ta yiwa kasar Iran.
A jiya Litinin ne bankin ANZ da ke kasar Australia, yayi hasashen cewa me yiwuwa farashin gangan mai ya kai dala dari nan ba da dadewa ba.